Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kebbi (KESIEC), ta bayyana ranar 31 ga watan Agusta a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansilolinsu a kananan hukumomi 21 na jihar.
Wata sanarwa daga hedikwatar KESIEC mai dauke da sa hannun shugaban hukumar, Hon. Aliyu Muhammad Mera, ya nuna cewa za a gudanar da zabe a ranar 31 ga Augustan wannan shekarar don takarar kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli 225 a fadin jihar.
- Sin Na Fatan Amurka Na Yin Wani Abun A-zo-a-gani Na Tallafawa Farfadowar Nahiyar Afirka
- Zimbabwe Ta Yaba Da Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Bangaren Makamashi Mai Tsafta Na Kasar
Hukumar ta sanar da cewa za a iya samun fom din tsayawa takara da juma tuntubar juna da duk wasu takardun da suka shafi zaben daga sakatariyar KESIEC da ke Birnin Kebbi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan don bai wa jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a damar fahimta tare da fara dukkan shirye-shiryen da suka dace dangane da zabe mai zuwa”.
Bugu da kari hukumar tana neman goyon baya da hadin kan masu ruwa da tsaki da sauran al’umma domin ganin an gudanar da zabukan kananan hukumomi cikin adalci da kuma gaskiya, don samun sahihin zabe da kuma zama karbabe ga jama’a a jihar.
Wakilan hukumar da jam’iyyun siyasa da tsaro da sauran masu ruwa da tsaki sun gudanar da taron tuntubar juna a Birnin Kebbi a wannan Juma’a domin isa ga ranar da aka amince da gudanar da zaben kananan hukumomin da duk wadanda suka halarta za su yi.