Gwamnatin jihar Katsina ta ce nan da kwanaki kadan masu zuwa, za ta bazama dazuka lungu da sako don fatattakar ‘yan bindigan da suka addabi Jihar.
Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Muktari Lawal, ne ya bayyana hakan a wajen bikin yaye ‘yan banga 600 da aka horas, ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka Daban-daban a jihar.
Lawal ya bayyana horar da ’yan banga a matsayin mafi kyawun irinsa, inda aka horas da su dabarun sarrafa makamai da dabarun kare kai don yakar ‘yan ta’adda.
Acewarsa, “Na ji dadi da aka ce in zo, zan koma gida tare da fata da karfin gwiwar cewa ‘yan ta’adda za su fita daga jihar Katsina.
“Ba ni da shakka a cikin raina cewa a cikin kwanaki masu zuwa zai zama mafi mawuyacin hali da ‘yan bindigar zasu fuskanta.
“Babu gudu ba ja da baya, babu mika wuya, za mu yi yaki da ‘yan ta’addan, Kuma za mu maida su inda suka futo har zuwa karshe.”