Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da tallafa wa Rundunar ’Yan Sanda domin inganta ayyukansu a faɗin jihar.
Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan, inda ya ce, Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin Sakataren Zartarwa na Hukumar Tallafa wa Harkokin ‘Yan Sanda ta Ƙasa (NPTF), a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa tawagar ta NPTF ta kai ziyara ne domin duba sabon barikin tagawar ‘yan sanda ta musamman da hukumar ta gina a jihar.
Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da niyyar haɗa kai da hukumar wajen inganta jin daɗin ‘yan sanda da kyautata yanayin ayyukansu.
Ya ce, “Gwamnatina na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an kula da walwala da jin daɗin ‘yan sanda. Wannan ne dalilin da ya sa muke gyaran hedikwatar ‘yan sanda ta Zamfara a halin yanzu.
“Haka kuma, muna gina wasu muhimman gine-gine a hedikwatar rundunar ‘yan sanda na Moble. Mun samu nasarori da dama a wajen, kuma muna da ƙarin shirye-shirye na gaba.
“Na ji daɗin yadda sakataren hukumar ya ambaci batun ginin sabon unguwar ma’aikatan ‘yan sanda. Idan ka duba halin da barikin ‘yan sanda ke ciki yanzu, za ka fahimci cewa abin ya fi ƙarfin misali.”
Gwamna Lawal ya ƙara da cewa, yana daga cikin kwamitin shugaban kasa kan sauya fasalin ‘yan sanda, inda ya bayyana yadda suka ziyarci makarantu da cibiyoyin horas da jami’an ‘yan sanda a jihohi daban-daban.
“Abin takaici ne yadda muke sa ran ‘yan sanda za su yi ayyuka masu girma, alhali suna fama da mummunan yanayin rayuwa. Ina daga cikin masu fafutukar ganin an sake fasalin tsarin walwala da albashin ‘yan sanda gaba ɗaya. Wannan dai lokaci ne kawai.”
Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta bayar da ƙasa domin gina sabon gidajen ‘yan sanda, yana mai cewa, “Ina farin ciki da kasancewar kwamishinan gidaje a nan tare da mu. Ya zama dole mu fara aiki da gaggawa wajen tantance filin da za a miƙa wa hukumar domin fara aikin.”
Tun da farko, Sakataren Zartarwa na Hukumar Tallafa wa ‘Yan Sanda, Mohammed F. Sheidu, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa haɗin kai da goyon baya da yake bai wa rundunar, musamman a bangaren walwala da gine-gine a Zamfara.














