Kamfanin da gwamnatin tarayya ta bai wa aikin kula da kwaskwarima na babban hanyar Bauchi zuwa Gombe, Anaco Nigeria Limited, ya sha alwashin gyara hanyar da ta yanke a daidai gadar Kaljanga cikin kwanaki uku masu zuwa.Â
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, a sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a safiyar ranar Lahadi wanda ya yi sanadin ruftawar gadar, lamarin da janyo raba jihohin da ke yankin arewa maso gabas daga zuwa sauran yankunan kasar nan.
Lamarin ya tilasta wa wasu matafiyan fasa tafiyar yayin da wasu kuma suka yi zagaye mai nisa domin samun damar zuwa wuraren da suke son zuwa.
Kodayake, kamfanin ya ce nan da kwanaki uku za su yi garanbawul ga hanyar ta yadda motoci za su samu damar wucewa.
Wakilinmu ya labarto cewa ba wannan ne karo na farko da hanyar Bauchi zuwa Gombe ke yankewa ba, sai dai ba a taba samun yankewar hanyar ba kamar na wannan lokacin.
Gwamna Bala Muhammad da ya ke maida jawabi jim kadan bayan wakilin kamfanin kwangilar ya bada tabbacin kammala kwaskwarimar cikin Kwana Uku, ya ce, wannan lamarin ya janyo kunci ga jama’a kuma zai shafi tattalin arzikin jama’a muddin ba a yi gaggawar daukar matakin gyara hanyar cikin kankanin lokaci ba.
Bala ya ce, hanyar ta gaji ne gaba daya ba ta bukatar wata kwaskiwarima, sake ginawa ne ya dace da ita.
Ya bukaci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta duba halin da hanyar ke ciki domin sake bayar da kwangilar sake ginawa, ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnatin baya ta Muhammadu Buhari ta yi watsi da hanyar duk da tsananin bukatar agajin gaggawa da hanyar ke bukata.