Gwamna Dauda Lawal ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar ban girma da Kwamandan hukumar NDLEA a jihar Zamfara ya kai gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Talata.
- Matar Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar Da Bada Tallafin N50,000 Ga Mata Dubu 4 A Gusau
- Cin Zarafi: Kungiyoyin Kwadago Za Su Tsunduma Yajin Aiki A Ranar 14 Ga Nuwamba
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, kwamandan ya nuna matukar damuwa dangane da yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar.
Sanarwar ta nanata kudirin gwamna Lawal na hada kai da hukumar NDLEA domin tabbatar da tsaftacce jihar daga ta’ammuli da miyagun kwayoyi.