Yayin da al’ummar Nijeriya ke ci gaba da kokawa kan matsalolin rashin tsaro, babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya (CDS), Janar Chris Musa, ya bayyana cewa rundunar sojin Nijeriya na shirin sauya salon ayyukanta na yaki da ‘yan ta’adda.
Ya ce, za su yi amfani da hanyoyin da suka da ce da za su kara wa jami’an sojin kaimi wajen magance rashin tsaro a fadin Nijeriya.
- PDP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Zaben Kaduna Da Ta Tabbatar Da Nasarar Uba Sani
- Maulidi: Gwamna Uba Sani Ya Bukaci Addu’o’in Zaman Lafiya Da Ci Gaban Kasa
Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya kai wa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ziyara a gidan gwamnati – Sir Kashim Ibrahim House.
Janar Musa ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Kaduna cewa, za a fadada ayyukan rundunar Operation Safe Haven da ke Kudancin Kaduna domin yakar ‘yan bindiga da ke yankin Birnin Gwari, Zangon Kataf, Sanga, Kaura da Giwa kamar yadda Gwamnan ya bukata.
A nasa jawabin, gwamna Uba Sani ya yaba da kyawawan ayyukan CDS Janar Musa, inda ya bayyana cewa, shi mutum ne jajirtacce wanda ya samu nasara a duk ayyukan da aka damka masa.
“Janar Musa, mutum ne amintacce a wurin mu, muna da yakinin cewa nan ba da jimawa ba batun rashin tsaro a Nijeriya zai zama tarihi sabida irin rawar ganin da ya taka a yaki da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.”