Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar za su tabbatar kudurin canza fasalin dokokin haraji da gwamnatin tarayya ta kai a majalisar kasa bai kai labari ba.
Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana cewar dokokin da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ke son kakabawa jama’a ba su dace ba, don haka ba za su goyi bayan su ba.
- Dokokin Gyaran Haraji Sun Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
- Babu Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Yaki Da Hauhawar Farashin Kayayyaki – CBN
Tsohon Gwamnan kuma jagoran jam’iyyar PDP a Sakkwato ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a karamar hukumar Shagari a yayin da yake kaddamar da tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa da hare – haren ta’addanci ya shafa a mazabarsa.
Tambuwal wanda ya shugabanci majalisar wakilai ta bakwai ya bayyana cewar al’umma suke wakilta a majalisa ba kan su ba kuma sun saurari ra’ayoyin jama’a wadanda suka nuna rashin gamsuwa da dokokin don haka ba za su yi abin da zai cutar da al’ummarsu ba.
“Kun zabe mu ne don mu kare muradun ku da ra’ayoyin ku don haka muna tabbatar maku cewar da yardar Allah za mu kai karshen wannan matsalar ta hanyar watsi da wandanan dokokin da ke a gaban majalisar dattawa da majalisar wakilai.”