Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina ta tabbatar da cewa za ta bi dukkan hanyoyin da suka dace don kare kuri’unta a zaben gwamna da ke tafe.
Daraktan yakin neman zaben Atiku/Lado na jiha, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya fadi hakan a lokacin taron manema labarai da ya gudana a ofishin yakin neman zaben jam’iyyar da ke Katsina.
- An Fitar Da Tsarin Yin Kwaskwarima Na JKS Da Hukumomin Gwamnati
- EFCC Ta Gurfanar Da Farfesa A Gaban Kuliya Bisa Zargin Damfarar N1.4bn
Dakta Inuwa ya yi nuni da cewa hakan ya zama wajibi don tabbatar da dakile magudin zabe da take zirgin jam’iyya APC da yunkurin yi.
Daraktan yakin neman zaben ya nuna rashin jin dadinsa bisa irin yadda jam’iyya mai mulki take yi wa ma’aikatan gwamnati barazana akan tilasta masu zabar dan takarar jam’iyyar gwamnati, inda ya bayyana hakan a matsayin yunkurin kassara dimokuradiyya.
Haka nan kuma ya jaddada cewa, Sanata Garba Yakubu Lado Dan Marke shi ne dan takararta na gwamna a zaben gwamnoni da za a yi.
Ya bayyana cewa wasu jami’yyun adawa ke yada jita-jitar da ke cewa Yakubu Lado ya janye takararsa don su bata masa suna, sai dai ya bayyana abun a matsayin zagon kasa ga jam’iyyar PDP.
Ya kuma karyata wasu labarai da ke cewa jam’iyyar ta yo hayar ‘yan daba daga jihohi makwabta domin kawo tarnaki ga zaben gwamna. Ya ce a ko da yaushe jam’iyyar PDP na gargadin magoya bayan ta da su kasance masu bin doka da oda don tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tsarin mulkin dimokuradiyya baki daya. Ya bukaci al’umma da su fito su kada kuri’arsu ga jam’iyyar PDP.