Bisa alkaluman da jami’ar John Hopkins ta kasar Amurka ta fitar, zuwa karfe 6 da minti 21 na yammacin jiya Laraba, agogon gabashin Amurka, jimillar mutanen da suka kamu da cutar mashako ta COVID-19 a kasar, ta zarce miliyan 90, kana, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar, ya zarce miliyan 1.02, wadanda dukkansu adadi ne dake kan gaba a duniya.
Me ake nufi da mutane miliyan 90 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19? Wato a cikin mutum 3.6 a Amurka, akwai guda daya da ya kamu da cutar. Kwararru da kafofin watsa labaran Amurka sun ce, mutanen kasar da yawa su kan yi gwaji da kansu a gida, ko kuma sam ba sa yi, al’amarin da ya sa yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a zahiri, ya fi abun da aka sani yanzu.
Tun farkon bullar cutar, mahukuntan Amurka sun raina hadarinta da gangan, haka kuma manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu suna ja-in-ja game da manufofin yaki da cutar.
Sa’annan a halin yanzu, gwamnatin tarayya gami da ta kananan hukumomin kasar, suna jan kafa wajen hana yaduwar cutar, al’amuran da suka sa mahukunta gazawa matuka wajen yaki da ita, inda kuma jama’ar kasar suka fi jin radadi a jikinsu.
Amurka kasa ce mafi karfin tattalin arziki a duniya, amma ta fi dukkan sauran kasashe muni wajen yakar annobar COVID-19, abun da ya shaida rashin aikin tsarin siyasa da rashin tafiyar da hakokin mulki yadda ya kamata, da bayyana ainihin halin ‘yan siyasar kasar, na sanya muradunsu a gaban rayuwar al’umma. (Murtala Zhang)