Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta bayyana cewa, jam’iyyar LP da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, sun gaza bayyana ikirarinsu na samun kuri’u masu rinjaye da aka kada a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A hukuncin da mai shari’a Abba Bello Mohammed ya karanto, ya ce jam’iyyar ta yi zarge-zarge da suka da ikirarin cewa, ba abin ka’ida, an yi aringizon kuri’u da kuma gudanar ayyukan cin hanci da rashawa domin karkatar da kuri’unsu, musamman a jihohin Ribas, Benue, Legas, Taraba, Imo da Osun amma ta gaza bayyana rumfunan zaben da duk wanna zarge-zargen nasu ya shafa.
Mai shari’a Mohammed ya ci gaba da cewa, LP kuma ta kasa tabbatar da zarge-zargen da ta ke yi wa jam’iyyar APC, da tulin kuri’un da ta ce an rage mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp