Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa sun ayyana shiga zanga-zangar kwana bakwai, inda suka bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta sake yin nazari kan sakamakon zaben gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Sun yi zanga-zangar ne a karkashin masu ruwa da tsaki na mambobin PDP da ke karamar hukumar Karu a jihar.
- CMG Ta Hada Kai Da Manyan Kafafen Yada Labaran Kasashen Afirka Biyar Don Kaddamar Da Wani Shirin TV Mai Suna “More Ci Gaba Tare”
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Equatorial Guinea
Sun bukaci a gaggauta cire kwamishin hukumar zabe na jihar, sun kuma soki hukumar ta INEC bisa nuna sin kai a lokacin zaben gwamnan da na ‘yan majalisar dokoki na jihar.
Masu zanga-zangar dauke da alluna sun nuna rashin jin dadinsu.
Kwamared Chindo Allahyayi ne ya kaddamar da zanga-zangar a karamar hukumar Karu, inda ya bukaci INEC da ta mayar da damar masu jefa kuri’a da ta murde ta kuma sanar da ainahin wanda ya lashe zaben na kujerar gwamnan jihar.
Chindoya kuma yi tir da magudin zaben da aka tafka a jihar, inda ya ce hakan ba zai haifar wa jihar da mai ido ba.
A cewarsa “Muna bukatar a je a duba manhajar tattara sakamakon zabe ta INEC domin a duba sakamakon zabe na daukacin mazabu da ke a kananan hukomomi 13, inda sakamakon ya nuna cewa, dan takarar gwaman a jihar na PDP, David Ombugadu ne ya lashe zaben.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, INEC ta sanar da sunan gwaman jihar, Abdullahi Sule kuma dan takara a jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben na gwaman jihar.