Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce ba ta bai wa jami’an tsaro shaidar yin aikin zabe da ke dauke da sunanta da hatiminta da nufin samun damar shiga aikin zabe ba.
Domin fayyace zare da abawa, hukumar ta ce, ba ta samar da kowace shaidar aiki ga wani jami’in tsaro ba, inda ta kara da cewa, hukumomin tsaro ne ke da alhalin samar wa jami’ansu shaidar yin aikin ba wai hukumar ba.
- Dandazon Jama’a Sun Fito Jefa Kuri’a A Zaben Gwamna A Bauchi
- An Samu Jinkirin Rarraba Kayan Zabe A Bauchi
INEC ta yi wannan ankarar ne a cikin wata sanarwar da shugaban sashin yada labarai na hukumar Barista Festus Okoye ya fitar a Abuja ranar Juma’a.
Okoye ya ce, duk wani jami’in tsaron da aka gani dauke da irin wannan shaidar zai iya zama haramtacciya.
Kuma ya ce, kama mutum da gurfar da duk wanda aka samu da irin wannan shaidar za a yi.
“Ana sanar da jama’a kan wannan aika-aika na wasu bata gari da sannan kuma su kai rahoto ga jami’an tsaro na irin wadannan jami’an da zarar suka gansu.”