Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC a Jihar Gombe, ya ce ya gano wasu bata-gari daga jam’iyyun adawa a jihar, na kitsa makarlashiyar bata sunan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, dan takaran gwamna a jam’iyyar a zabe mai zuwa.
A wata sanarwar da Ismaila Uba Misilli, Daraktan yada labarun kwamitin yakin neman zaben APC A Jihar Gombe, ya ce, “Sahihan bayanai sun yi nuni da cewa wadannan ‘yan adawar su na aika-aikar su ne karkashin masu basu na goro don neman bata suna da karya lagon dan takaranmu da sauran jiga-jigan jam’iyyar domin su yaudari al’ummar Jihar Gombe wadanda tuni suka yanke shawarar sake zaben Gwamna Inuwa a karo na biyu.”
- Siyasar Bauchi: ‘Yansanda Na Neman Dan Majalisar Tarayya, Yakubu Shehu Ruwa A Jallo
- Na Kalubalanci Tsarin Da Ya Ayyana Tinubu A Matsayin Shugaban Kasa -Peter Obi
Ya kara da cewa, “Ganin yadda suka tabbatar cewa ba za su yi wani katabus a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisan jiha da za a yi a ranar 18 ga wannan wata na Maris ba, wadannan makiya na Jihar Gombe sun dauki aniyar aiwatar da mummunan makircin su don ganin hakar su ta cimma ruwa.”
“Mu ‘yan kwamitin yakin neman zaben Jam’iyyar APC a Jihar Gombe mun ga ya dace mu jawo hankalin al’ummar jihar tare da yin kira a gare su, su yi watsi da duk wani makirci irin wannan.”
Ya jaddada cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya tsaya tsayin daka da jajircewa wajen ci gaba da gudanar da mulki na gari don ingantuwar Gombe ga dokacin al’ummar jihar da kewaye.
“Muna kira ga al’umma kar irin wannan zagon kasa da farfagandar siyasa na ‘yan adawa ya rude su, wadanda ke barazana ga zaman lafiyarmu.”
Ya ce, Gombe ta yi suna a fagen zaman lafiya da siyasa mai tsabta. Don haka dole ne suke fatan gudanar da harkokin zabe a matsayin ‘yan uwa ba tare da nuna kyama ko son zuciya da da”cin rai ba.
“Haka nan muna gargadin masu kitsa irin wannar makarkashiya da aika-aika, su shiga taitayin su, domin al’ummar Jihar Gombe su na goyon bayan Gwamna Inuwa Yahaya kuma da yardar Allah zasu ba shi damar yin wa’adi na biyu a ranar Asabar 18 ga wannan wata.”