Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta amince da bukatar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi na sake inganta na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) da aka yi amfani da ita wajen gudanar da zaben shugaban kasa da aka kammala a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Mai shari’a Joseph Ikyegh ya ce alkalan zaben sun ba su tabbacin cewa, an daura bayanan da ke cikin na’urar BVAS a cikin rumbun adana bayanai na hukumar INEC domin samun tsaro mai aminci.
Har ila yau, kotun ta amince da bukatar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na duba kayan zaben da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, dan takarar jam’iyyar Labour (LP) a zaben shugaban kasa, Peter Obi da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun shiga dakin kotun sauraren kararrakin zaben domin shaida yadda kotun za ta yanke hukuncin bukatun da aka kai gabanta.
Acikin tawagar da suka raka Obi kotun, akwai shugaban jam’iyyar na kasa, Mista Julius Abure, Sanata Victor Umeh da sauran su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp