Kasar Sin, kamar ragowar kasashe na da ikon zabar hanyoyin raya kanta bisa yanayin da take ciki, don haka, bunkasuwar kasar, kamar yadda ta sha nanatawa a mabambantan lokuta cewa, har kullum buri da manufar kasar Sin, shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiyar duniya baki daya, sabanin yadda wasu kasashe ke kallonta da ma yada jita-jitar cewa, wai ci gaban kasar Sin, musamman kokarin da take na zamanantar da kanta, baraza ce ga duniya.
Sanin kowa ne cewa, kasar Sin na da dabaru da fasahohi masu kyau a fannin ingiza zamanintarwa da hadin kan kasa da kasa, da sa kaimi ga canja salon makamashi, kuma dukkansu abin koyi ne ga kasashen duniya. Amma wasu kasashe na nuna kishi da ci gaban kasar Sin, inda suke kokarin yiwa wannan ci gaba bahaguwar fahimta tare da neman hana ci gabanta ta kowa ne hanya.
Kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin kawar da talauci, da raya masana’antu, da yin amfani da sabbin fasahohi, kana tana da gogewa masu tarin yawa, da za ta iya rabawa ga duniya. Don haka sauran kasashe za su iya koyo da ma cin gajiya daga zamanantarwa irin na kasar.
Masu fashin baki na cewa, akwai bukatar kasashe su koyi kyawawan manufofi da ayyukan juna, yadda kasar Sin take da kwarewa da kuma musayar gogewarta, babu shakka zai taimakawa kasashe, musamman masu tasowa wajen zabar salon zamanintarwa da zai dace da yanayin kasashensu da kuma biyan bukatunsu.
A matsayinta na kasar da ta san ya kamata, Sin tana hadin kai da kasashe mambobin MDD don aiwatar da shawarar raya duniya baki daya, da kafa tawagar sada zumunta wajen aiwatar da shawarar a dandalin majalisar. Shawarar da ta nuna kyakkyawan fata da alkawarin da kasar Sin ta yi wajen inganta ci gaban duniya.
Har kullum kasar tana fatan kasashen yammacin duniya, musamman Amurka da sauran kawayenta za su kalli ci gabanta, da kokarin da take na zamanantar da kanta da idon na basira, ta yadda za su dakatar da yada farfaganda maras tushe, ta daukar wannan manufa da masu fashin baki ke cewa, za ta amfani duniya a matsayin barazana.
Hanya mafi dacewa ta warware dukkan batutuwa da suka shafi kasashen duniya, musamman a wannan lokaci da duniya ke bukatar zaman lafiya, adalci ita ce tattaunawa, maimakon ware kai, da mayar da wasu saniyar ware, da gudanar da komai a bayyane, da damawa da kowa da kowa bisa daidaito da mutunta juna, tare da ci gaba da shawarwari da yin hadin gwiwa, maimakon yada zarge-zarge marasa tushe. Amma zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ko ana shafo sai ya yi.