Kasar Sin ta sha nanatawa a dandali da taruka daban-daban cewa, buri da manufar kasar a kullum, shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiyar duniya baki daya, sabanin yadda wasu kasashe ke kallo da ma yada jita-jtar cewa, wai ci gaban kasar Sin, barazana ce ga duniya. Sanin kowa ne cewa, kasar Sin ba barazana ba ce ga duniya.
Wannan ne ma ya sa kasar Sin ke fatan musamman Amurka da sauran kawayenta, za su rika yiwa ci gaban Sin kallo na idon basira, ta yadda za su dakatar da yada farfagandar nan maras tushe ta daukar ci gaban Sin a matsayin barazana.
Batu na baya-bayan nan shi ne, na bala-balan din farar hula na kasar Sin da iska ta kada shi samaniyar Amurka bisa kuskure, inda Amurka ta ke neman siyasantar da batun, tare da neman wasa da hankalin jama’a, da kokarin bata sunan kasar Sin. Kuma matakan da ta dauka, sun sabawa yarjeniyoyin kasa da kasa. Kasar Sin dai ta yi Allah wadai da wannan mataki na Amurka. Kasar Sin kasa ce mai kaunar tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Sanin kowa ne cewa, hanya mafi dacewa ta warware duk wasu batutuwa da suka shafi kasa da kasa, ita ce tattaunawa da dukkanin kasashe masu ruwa da tsaki, maimakon ware kai, da mayar da wasu saniyar ware, da zage damtse wajen gudanar da komai a bayyane, da shigar da kowa, tare da ci gaba da shawarwari da hadin gwiwa, maimakon yada zarge-zarge marasa tushe.
Bugu da kari, shata layi saboda bambancin akida, da hada wata tawagar nuna wariya kan wasu kasashe, da yayata manufar ware kai tare da ’yan kanzagi, duk sun sabawa akidun zamanin yau, kuma ba za su yi wata nasara ba.
Ya kamata a fahimci cewa, yanzu zamani ne na cude-ni-in-cude-ka, da martaba ka’idoji da dokoki na kasa da kasa da duniya ta amince da su, sabanin kokarin da wasu ke yi na nuna fin karfi ko dannayi, ko safawa saura bakin fenti, ko neman zama mai son kakabawa sauran kasashe ka’idoji na tilas.
Don haka, ya dace a rika martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa, maimakon fakewa da wani batu na siyasa ko wata manufa da nufin cimma wata moriya ko neman tayar da fita a sauran kasashe. Zama lafiya ya fi zama dan Sarki. (Ibrahim Yaya)