Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce zamanintarwa iri na kasar Sin za ta samar da taimako mai karfi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, da samar da muhalli mai fadi na raya wayewar kan bil Adama da ba da gagarumar gudunmuwa ga samar da ci gaban bil Adama, mai dorewa.
Wang Wenbin, wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Juma’a, ya ce rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, ya sanar da cewa, hanyar da kasar ta zaba ta zamanintar da kanta, za ta inganta gagarumin aikin farfado da al’ummar Sinawa.
Ya ce zamanantar da daukacin al’ummar kasar Sin sama da biliyan 1.4, za ta samar da wani kuzari da ba a taba gani ba ga ci gaban duniya.
Har ila yau, ya ce kasar Sin ta zamanatar da kanta ne ta hanyar neman ci gaba bisa la’akari da yanayinta, lamarin dake nuna cewa, babu wata hanya daya tilo ta zamanantar da kasa.
A cewar kakakin, abu ne mai yuwuwa ga kasashe masu tasowa, su lalubo hanyar samun ci gaba da ta dace da su, yana mai cewa, zamanantar da kasa ba dama ce da wasu tsirarun kasashe ne kadai za su iya mora ba, inda ya ce kamata ya yi ta kasance ‘yancin da kowacce kasa za ta iya samu ta hanyar kokari tukuru ba tare da gajiyawa ba. (Fa’iza Mustapha)