Cikin jawabin da ya gabatar ranar 20 ga watan Mayu, Lai Ching-te, ya yi amfani da kalmar “demokradiyya” wajen biyan bukatun Amurka da ‘yan siyasar yammacin duniya masu kin jinin kasar Sin, yana neman karin goyon baya da tallafi daga kasashen waje. Sai dai, duk yadda ya kawata batun, ba zai iya sauya ainihin gaskiyar cewa, Taiwan yanki ne na Sin ba.
A shekarar 1971, yayin zama na 26 na babban taron MDD aka zartar da kuduri mai lamba 2758, wanda ya warware batun wakilcin dukkan kasar Sin, ciki har da Taiwan, ta fuskar siyasa da tsari da ma dokar MDD. An fayyace cewa, kujera daya kadai Sin take da ita a MDD, kuma manufar kasar Sin daya tak ta zama matsayar da kasa da kasa suka aminta da ita, kana ita ce ka’idar huldar Sin da kasa da kasa.
Duk yadda mutane irin Lai Qing-te ke da alaka da wasu daga kasashen waje, ba za su iya hana dunkulewar dukkan yankunan kasar Sin ba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)