Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta kaddamar da fara bin diddigin dan kwangilar da ke kula da aikin madatsar ruwa ta Dawaki a karamar hukumar Kanke ta jihar Filato.
An yi zargin cewa dan kwangilar ya hada baki da wasu ma’aikatan gwamnati sun karbi naira miliyan 55 ba tare da yin komai a wurin aikin ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoto kan aikin bin diddigin aikin (Phase 1V) wanda jaridar Daily Trust ta samu kwafinsa a ranar Talata.
Rahoton ya bayyana cewa: ‘’An gano halin wasu ‘yan kwangila da za a basu kwangilar ayyuka amma ba za suyi komai ba, sai su karkatar da kudaden zuwa amfanin kawunan su”
Hukumar ta ICPC ta ce ta kuma fara damke wasu jami’an gwamnati da ke karkatar da kayayyakin da ake tanada don tallafawa al’umma.