Ma’aikatar tsaron kasar Zambiya ta gudanar da wani gagarumin bikin bayar da lambar yabo ga tawagar likitocin kasar Sin karo na 25 a Lusaka, babban birnin kasar, inda aka karrama mambobin tawagar su 11 da lambar yabo ta “hadin gwiwar kasashen waje” wato “Medal of Foreign Cooperation” a Turance.
A jawabin da ya gabatar yayin bikin, babban sakatare a ma’aikatar tsaron kasar Zambiya Norman Chipakupaku, ya yabawa kasar Sin bisa tura manyan likitocin da suke da kwarewa. Yana mai cewa Zambia za ta ci gaba da mutunta gudummawar da suke bayarwa da ma ilmin da suka kawo.
A cewarsa tawagar likitocin na kasar Sin sun kara bayar da gudummawa matuka ga lafiyar al’ummar Zambiya, kuma kwarewarsu ta likitanci ta sa jama’ar kasar da dama amincewa da su. Dalilin da ya sa suka ci gaba da samun yabo daga jama’a daga kowane bangare na rayuwa a kasar Zambia.
Ya ce Zambia, ta yaba da matakin hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya tsakanin kasashen biyu, kuma tana da niyyar kara karfafa ta zuwa fannonin kayayyakin aikin likitanci, da fasahohi da horarwa. Ya kuma yabawa tawagar likitoci da kasar Sin ta tura karo na 25 bisa kwazonsu. Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Zambiya na fatan zuwan tawagar likitocin kasar Sin karo na 26, tare da fatan sabuwar tawagar za ta daukaka al’adar tawagar mai barin gado.
A nasa jawabin babban jami’in hulda da jama’a na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Zambiya, babban kanar Jiang Lei, ya yabawa tawagar bisa ga dabbaka akidar tawagar likitocin kasar Sin, wadda ta kai su ga samun nasarar kammala aikinsu a cibiyar kula da lafiya ta Maina Soko da aka tsugunar da su. (Ibrahim Yaya)