Gwamna Dauda Lawal ya bukaci a kara kaimi wajen addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya a daidai lokacin da kasar ke bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Jihar Zamfara na cikin jihohi shida da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta kafa a ranar 1 ga Oktoba, 1996.
- Yawan Lantarki Da Makamashi Mai Tsafta Ke Samarwa A Sin Ya Karu
- Gwamnatin Kaduna Ta Raba Wa Manoma Taki Buhu 120,000
Gwamna Lawal, a cikin wani sakon fatan alheri da sakataren yada labaran gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Talata, ya ce, ranar 1 ga watan Oktoba rana ce ta musamman domin yin tunani a kan irin gwagwarmaya da sadaukarwar da tsoffin shugabannin Nijeriya suka yi don tabbatar da ‘yancin kasar da hadin kanta.
Ya kara da cewa, “a jihar Zamfara, bikin murnar bukukuwa biyu ne, kamar yadda muke gudanar da bikin cika shekaru 28 da kafuwar jiharmu da shekaru 64 da samun ‘yancinmu.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ya dace mu yi tunani da la’akari mai zurfi kan wannan mawuyacin hali da jihar Zamfara ke ciki, wanda ba a taba ganin irinsa ba, kama daga bangaren rashin tsaro, fannin lafiya da ilimi, da matsalar abinci, da lalata ababen more rayuwa.
“A cikin shekara guda na gwamnatinmu, jihar ta samu gagarumin sauyi kuma tana kan hanyar ci gaba.
“Muna samun ci gaba sosai a fannin tsaro, noma da samar da abinci, kiwon lafiya, fannin ilimi, samar da ababen more rayuwa, da sake fasalin ayyukan gwamnati da dai sauransu.
“Duk wadannan ana samun su ne duk da karancin albarkatun da jihar ke samu. Manyan abubuwan da aka samu na wasu nasarorin sun yi daidai da ajandar ceto jihar daga mawuyacin halin da ta tsintsi kanta yanzu”