Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kara nanata shirin da yake da shi idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2023, zai sayar da matatun man fetur ga ‘yan kasuwa.
Atiku ya shelanta hakan ne a wata hira ta musamman da sashen 5hausa na Muryar Amurka (VOA) ta yi da shi, a yayin da ya kai wata ziyara birnin Washington DC da ke Amurka.
- An Fara Rangadin Nuna Kashi Na Uku Na Fina-Finan Kasar Sin A Afirka
- ‘Yar Nijeriya Ta Zama Birgediya-Janar Din Sojin Amurka
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce, “Matsayina a kan wannan batun ba na yau bane, domin ko a shekarun baya, na furta cewa, zan sayar da matatun man future din kasar nan, domin idan aka sayar da su ga ‘yan kasuwa, za su fi tafiyar da su yadda ya dace”.
Da yake yin tsokaci akan satar man da ake yi a kudancin kasar nan, Atiku ya ce, ya yi alkawarin magance kalubalen, idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
A cewar Atiku, “Wannan wata matsala ce da ban da muka gani, mu ma za mu yi amfani da karfin iko don dakatar da satar man idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa.
Atiku ya kara da cewa, “Dole ya kasance akwai hadin kai a tsakanin kamfanin NNPC da hukumomin tsaro wadanda kuma ke da alhakin bai wa bututun man fetur na kasar kariyar da ya dace.”
Dan takarar ya bayyana cewa, Nijeriya na da matatun mai guda hudu na Kaduna, Warri da na garin Fatakwal wadanda dukkan su ba sa yin aiki kamar yadda ya kamata, inda ya kara da cewa, hakan ya janyo akasarin man da ake sarrafawa a ketare ne ake shigo wa da shi cikin kasar nan.