A watannin da suka gabata Nijeriya ta fuskanci kalubalen lalacewar rashin samar da wutar Lantarki na kasa tare da kuma fuskantar barazanar shiga yajin aikin ma’aikatan da ke a kamfanin samar da wutar na kasa, inda hakan ya janyo Nijeriya ta shiga cikin duhu saboda rashin wutar ta lantarkiÂ
Sai dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shelanta cewa, idan ‘yan Nijeriya suka zabe shi, tabbas gwamnatinsa za ta kawo karshen kalubalen da Nijeriya ke fuskanta na rashin wutar a kasar a 2023.
- Ruwan-wuta: ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Kubutar Da Dabbobi 110 A Katsina
- Ana Shirin Fadada Layukan Dogo Na Karkashin Kasa Dake Birnin Beijing
Atiku a cikin wata gajeriyar sanarwar da ya rubuta da hannunsa ya kuma fitar ya ce, bayan lurar da ya yi a halin da samar da wutar a cikin awa hudu, Gwamnatin na za ta lalubo da mafita kan rashin samun wadataciyar wutar a Nijeriya
Ya ci gaba da cewa, da farko zai cire fannin daga cikin manyan ayyukan kachokam ya kima mila wa jihohin kasar nauyin samar da wutar da kima rabar da ita a Jihohin su.
Ya kara da cewa, rikici a tsakanin Gwamnatin Tarayya da masana’antu, ba zai shafi samar da wutar a Jihohin Legas, kano, Abuja ko Abia ba ciki har da talakan Nijeriya da ke da bukatar wutar don amfanin sa ma yau da kullum.
Atiku ya ce, na biyu zan fito da tsarin bayar da damar zuba jari a fanin tare da bunkasa fannin, inda kuma gwamnati na za ta sa ido a kan tsarin da tabbatar da anyi komai yadda ya dace.
A cewarsa, buri na na son in zama shugaban shine in kare muradin talakan Nijeriya a ko wanne hali, saboda ina son in bayyana cewa, kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba, ba ni da ra’ayi ga wani kamfani da ke kira Janareto kamar yadda wasu suke yin jita-jitar ina da shi.