Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da shugabannin kungiyoyin kwadago ta kasa a fadar gwamnati da ke Abuja a yammacin ranar Laraba.
Kungiyoyin da suka hada da kungiyar kwadago ta ma’aikata NLC da takwararta ta ‘yan kasuwa TUC sun jagoranci zanga-zangar da aka gudanar a fadin Nijeriya a safiyar ranar Laraba, sakamakon cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi ba tare da samar da kyakkyawar mafita ba da za ta rage radadin cire tallafin ba.
Cire tallafin man fetur din da aka yi tun a ranar 29 ga watan Mayu, ya haifar da tsadar rayuwa da wahalhalu ga ‘yan kasa, musamman masu karamin karfi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp