A kowancce kasa da ke gudanar da Mulkin Dimkoradaiyya, hakki ne ga ‘yan kasar su gudanar da zanga- zangar lumana, domin su bayyana ra’ayinsu, da isar da bukaun su, ga Gwamnatin kasar, da suka son ta duba, wanda hakan ke ba su damar, jan hankalin Gwamnatin kasar, domin a samar da wani samar da sauyi, da suke bukata.
Hatta shi wannan ‘yancin, a rubuce yake a cikin kundin tsarin mulkin kasar.
- Tuƙin Ganganci: Direba Ya Kashe Jami’in KAROTA
- Yayin Da Ake Fuskantar Daminar Bana: Sabbin Hare-hare Na Barazana Ga Shirin Wadata Kasa Da Abinci
Sai dai, duk da cewa, Nijeriya da ita ma da ke bin tsarin Mulkin Dimokiradiyya, neman ‘yancin na Nijeriya, ya kasancen akasin haka, domin a duk lokacin da ‘yan kasar suka gudanar da wata zanga-zanga, musamman ta lumana, sukan fuskanci fishin hukuma ne, musamman jami’an tsaro irinsu ‘yansanda, da suke auka masu ko dai su kama su, su ci zarafin su, ko kuma su sha na Jaki, a hannun su.
Irin wannan zanga-zangar, ta sha ban-ban, da irin wadda ake gudanawar a kasashen da suka ci gaba kuma suke gudanar da mulki, irin na Dimokiradiyya, kamar da kasar Amurka, Birtaniya, Isara’ila da sauransu.
Sashe na 40, na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, ya bai wa ‘yan kasar ikon haduwa a waje guda su kuma yi hudda da sauran jama’a.
Kazalika, sashe na 11 na yarjejeniyar nahiyar Afirka, da ke magana kan ‘yancin ‘bil’Adama, wanda ita kanta Nijeriya ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar na barin ‘yan kasar su gudanar da zanga a cikin lumana.
Amma sai dai, abin takaicin duk da ‘yancin na wannan sashen, mahukunta Nijeriya, suna yawan take wannan ‘yancin, kan fakewa da cewa, suna tabbatar da bin doka da oda ne.
Misali, zanga-zangar #EndSARS, da ka yi a ranar 20 ga watan Okutobar 2020, da wasu matasan kasar suka gudanar a wasu titunan kasar, na a kawo karshen zaluncin da jami’an ‘yansanda ke yi, ta hanyar yakar masu yin fashi da makami da bukatar a inganta albashin ‘yansandan kasar, tare da kuma bukatar gwamnatin ta samar da wasu sauye-sauye.
Sai dai, zanga- zangar ta #EndSASR, da matasan suka gudanar a yankin Lekki ‘yansandan da aka tura zuwan wajen gudanar da zanga-zangar, sun rikidar da ita, ta zuwa nau’in yin amfani da Barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zangar, wadda har suka yi amfani da bindigunsu, da ke dauke da Albarusai masu aiki, wajen bude wuta kan masu zanga-zangar, don su tarwatsa su, wanda har aka yi zargin, a lokacin, wasu masu zanga-zangar, sun rasa rayukansu.
Har zuwa yau, babu wani babban jami’in dansanda da aka dora laifin aikata wannan laifin, hasali ma, gwamnatin waccan lokacin, karyata wa ta yi, na cewa, an sanu rasa rai, a lokaci zanga-zangar.
Sai dai, sarkakiyar aukuwar wannan lamarin, abu ne, da har yanzu, ke ci gaba da zama a zuciyar alummar kasar.
Bayan korafe-korafen da suka biyo bayan aikata nau’in zaluncin na ‘yansanda, hakan ya tilasta gwamnatin waccan lokacin, rusa jami’n na #EndSARS.
Tun bayan rusa jami’an na #EndSARS, ‘yan Nijeriya sun yi tsammanin hukumomin tsaro, za su sauya takun su na kwantar da zanga-zangar lumana a cikin ruwan sanyi, amma har yanzu, hakan ba ta sauya Zani ba.
Babbban misali shi ne, zanga-zangar da wasu ‘yan Nijeriya suka yi a 2024, cikinsu har da kananan yara, na gwmnatin ta kawo karshen matsin tattalin arziki da, musamman talakwan kasar ke ci gaba da fuskanta, jami’an tsaro sun kama wsu su da dama tare da kuma tsare su a gidan Yari, bissa tuhumar su, da cin amanar kasa.
Sai dai, kiraye-kiraye suka yi yawa ne, gwamnatin ta ga uwar bari, ta janye tuhumar da cin amanar kasa ta kuma sako su.
Bugu da kari, zanga-zangar lumana a kwanan baya da Mista Omoyele Sowore,ya jagoranta wadda ake a turance, ake kira da ‘Take-it-Back Mobement’, a nan ma jami’an tsaro, sun tarwatsa ta hanyar yin amfani da Hayaki mai sanya Hawaye.
Wani abinda ke daure kai shi ne, a duk lokacin da masu zanga-zanga suka nuna goyon bayan wasu tsare-tsaren gwamnati, ba bu wani jami’in tsaro da ke auka masu.
Kazalika, wani lokacin gwamnati ta kan dauki nauyin wasu ‘yan bangar siyasa da ke gayon bayan ta, domin su aukawa masu zanga-zangar adawa da ita, koda kuwa, an tura jami’an tsaro wajen zanga-zangar, sai su burus su kyale, a ci zarafin su.
Irin wannan matakin na gwamnatin, ya nuna a zahiri, yazama na taka doka da oda da gwamnat ke yi, na tauye barin ‘yan kasar su fadi ra’ayinsu.
Sai dai, a lokacin tsohowar gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta kasance ta bai wa ‘yan kasa damar yin zanga-zanga domin fadar ra’ayoyinsu, kan tsare-tsaren gwamnati, da suka ganin, ba su yi masu dadi ba.
Muna sane da rawar da Shugaban kasa mai ci, Ahmed Bola Tinubu, ya taka, kan zanga-zangar 2012, da a turance ake kira da ‘Occupy Nigeria’, da aka shafe mako daya ana gudar da ita, har ta kai ga ta janyo harkar kasuwanci ta tsaya cak a Legas, da sauran sassan Nijeriya, wadda manufarta shi ne, yaki da cire tallafin mai.
Hakazalika, tsohuwar minister Dakta Oby Ezekwesili ta jagoranci zanga-zangar ‘BringBackOurGirls’ (BBOG), inda suma wasu ‘yan Nijeriya, suka gudanar da irin wannan zanga-zangar, har ta kai tsawon kusa shekaru biyu a jere, ana guidanar da ita, domin su tilatawa gwamnatin ta kubutar da ‘yan matan na makarantar Chibok,
Zanga-zangar kwanan baya da miliyoyin Amukawa suka gudanar ta wadda kuma ta karade birane 1,000 na jihohi 50 na kasar, domin nuna adawarsu da tsare-tsaren gwamantin, ba bu wani jami’in tsaro da ya yi amfani da Albushi, ko Barkon tsohuwa kan masu zanga-zangar
Haka irin wannan batun yake a kasar In Isra’ila, musamman duba da zanga-zangar adawa ta kwana biyar da Isa’ilawa suka yi a 2023 kan sauye-sauyen da Faramintan kasar Benjamin Netanyahu, ya kirkiro da su a bangaren Shari’a, wanda gwamnatin ba ta matsawa masu zanga-zangar matuka ba, kuma ta tabbatar da an girmma ‘yancin masu gudanar da ita.
Abin tambayar a nan shi ne, mai ya sa a Nijeriya zanga-zangar lumana take komawa fagen jan daga a tsakanin masu gudanar da ita, da kuma jami’an tsaro?
Daya daga cikin amsar ita ce, salo ne kawai na gwamnati, na son tauyen hakkin ‘yan kasar, mai makon barinsu, su fadi ra’ayinsu.
Wannan dai, wani abu ne mai hadarin gaske, ba wai kawai na tauye masu hakkin ba, har da janyo Dimokirayya babban nakasu.
Dimkiradiyya ba wai kawai batun kada Kuri’a ba ne, amma akwai bukatar gwamnati, ta rinka sauraron ra’ayoyin ‘yan kasa, domin kuwa zanga-zangar lumana, na daya daga cikin bangaren da ‘yan kasa za su samu saurin isar da sakon su, ga gwamnati.
Wannan Jaridar na shawartar gwamnatin shugaba Tinubu, da ta bode kofar tattauna wa masu zanga-zangar lumana, daidai da tsarin Dimkaradiyya, mai makon yi masu barazana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp