A makonnin da suka gabata ne, wani fitaccen Malamin addinin Musulunci mai suna Malam Lawan Shuaibu Abubakar wanda aka fi sani (Abubakar Triumph), a jihar Kano, wasu daga cikin karatuttukansa suka fara tayar da ƙura a shafukan sada zumunta, inda al’ummar Musulmi musamman daga ɓangaren ɗariƙun sufaye, suka zargi malamin da ɓatanci ko ƙasƙanta darajar Annabi Muhammad SAW.
Wannan zargin ya haifar da cece-kuce da rashin jituwa a tsakanin mabiya addinin Musulunci, inda wasu daga cikinsu, musamman a ɓangaren ƙungiyar Izala (JIBWIS) suka goyi bayan fatawar Malamin da cewa, ba a yi masa kyakkyawar fahimta ba, ba yana nufin asalin abin da ake zargin malamin da shi ba ne.
- Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza
- Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa
Lamarin dai ba sauƙi ya yi ba face ƙara ta’azzara, inda ya haifar da zanga-zangar ƙin amincewa da karatun Malamin, inda daga bisani masu zanga-zangar suka kai ƙorafinsu gidan gwamnatin jihar ta hanyar ofishin sakataren gwamnati.
Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka zayyana sun haɗa cewa, ya danganta halittar Annabi SAW da ƙasƙantun halittu (‘Ya’yan Tumkiya, da Karya, da Ƙwarƙwata), sannan kuma ya taɓa alfarmar iyayen Annabi SAW wanda a cewarsu, hakan bai dace ba a alfarmarsa fiyayyen halitta.
Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba tare da ɓata lokaci ba, ta miƙa koken ga Majalisar Shura ta jihar domin fayyace gaskiyar lamari.
Majalisar Shura, ta bakin Sakatarenta, Shehu Wada Sagagi, a wani taron manema labarai da ta gudanar, ta tabbatar da cewa, za ta gudanar da cikakken bincike akan zargin da aka yi wa Malamin (Abubakar Triumph). Sannan kuma, za ta gayyaci masu ƙorafe-ƙorafe da kuma Malamin domin sauraron bayanansu. Ya ce matakin zai bai wa kowanne ɓangare dama kuma za a bi ƙa’idojin shari’ar Musulunci wajen gudanar da binciken.
Sagagi ya roƙi jama’a da su zauna cikin kwanciyar hankali, tare da jaddada muhimmancin kiyaye zaman lafiya da Kano ta yi fintinƙau akai. Ya tabbatar da cewa, majalisar za ta yi bincike da tattaunawa kafin ta bai wa gwamnati shawara kan matakin da ya dace bisa ga ƙa’idar shari’a.
Daga bisani kuma, rahotanni sun bayyana cewa, Majalisar ta dakatar da Malam Abubakar Triumph daga yin wa’azi a jihar har sai ta kammala bincike.
Ta kuma yi gargaɗi ga ‘yan siyasa da su guji tsoma baki a lamarin, inda ya jaddada buƙatar barin Majalisar ta kammala aikinta cikin gaskiya da adalci.
Ranar da aka daɗe ana tsumayi, ranar zaman tattaunawa da Malam Triumph da masu sukar kalamansa, ta tabbata inda aka yi zama a ofishin Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke Kano a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoban 2025.
An gudanar da taron ne ƙofa rufe, inda mambobin Majalisar suka shawarci malamin da ya riƙa yin taka-tsantsan da natsuwa a cikin bayanansa na addini. Rahotanni sun nuna cewa, malamin ya nemi afuwa a yayin tattaunawar.
Bayan kammala zaman, Malam Triumph ya wallafa kalmar “Alhamdulillah” a shafinsa na Facebook abin da jama’a da dama suka fassara a matsayin alamar cewa an kammala zaman lafiya tsakaninsa da Majalisar Shura, amma dai, al’umma musamman masu ƙorafi suna nan suna jiran sakamakon zaman tattaunawar daga bakin gwamnatin Kano.
Ko ina aka kwana? Majalisar Shura ba ta miƙa sakamakon zaman ba ne ga gwamnatin Kano ko kuma gwamnatin ce ta yi biris?
Don jin wannan amsar ne, masu ƙorafi a ƙarƙashin ɗariƙun sufaye suka maka gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da kwamishinan ‘yansanda na jihar a kotu kan zargin cewa, sun ƙi gudanar da haƙƙin da ya rataya a kansu kan cafke wanda ake zargi da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.
An ga matakin kotun ne a wata takarda da aka yada a kafafen sada zumunta, mai taken “Dambarwar Shari’a a cikin batun Malam Abubakar Lawal (Lawan Triumph) a Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Kano.”
A cewar takardar, waɗanda ake ƙara da suka haɗa da Gwamna Yusuf, Kwamishinan ‘Yansanda, da Babban Lauyan gwamnati, an zarge su da gazawa wajen aiwatar da ayyukansu na doka na gurfanar da masu aikata manyan laifuka a ƙarƙashin Dokar Shari’a ta Jihar Kano ta 2000 da Dokar Laifukan Intanet ta 2024 (wadda aka yi wa kwaskwarima).
Ƙungiyoyin da suka yi haɗin gwiwar shigar da ƙarar sun haɗa da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative, Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’isa, Ashabul Kahfi Foundation, da Majmau Ashabul Yameen.
Har zuwa lokacin rubuta wannan nazari, gwamnatin Jihar Kano ko rundunar ‘yansanda ba su bayar da wani martani a hukumance kan ƙarar ba.














