Yau ake sa ran EFCC za ta gurfanar da tsohon Akanta-Janar, Ahmed Idris, a gaban babbar kotu a Abuja, domin fara yi masa shari’a kan zargin almundahana da hukumar ke yi masa.
A wata sanarwa da kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya ce za a gurfanar da tsohon Akantan tare da wasu mutum biyu, Godfrey Akindele, da Mohammed Usman na kasuwar ‘Gezawa Commodity Market and Exchange Limited’ bisa zargin almundahana da yin sama da fadi da Naira biliyan 109.
- Mataimakin Kwanturola Da Ke Kula Da Gidan Yarin Kuje Ya Rasu
- Zaben 2023: Kwankwaso Ya Cancanta Ya Shugabanci Nijeriya -Zakiru Kusfa
Idan ba a manta ba, a watan Mayun da ya gabata ne EFCC ta kama babban Akanta-Janar din bayan ya ki amsa gayyatar da hukumar ta rinka aike masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake masa.