Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga kungiyar likitocin Nijeriya (NMA) reshen jihar Kano da ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma domin kaucewa jefa rayukan al’ummar Kano sama da miliyan 20 cikin hadari.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Gwamna Yusuf ya kafa kwamitin bincike kan zargin cin zarafin da kwamishiniyar jin kai ta jihar, Amina Abdullahi ta yi wa wata likita a ranar Litinin a asibitin kwararru na Murtala Muhammed.
- Tashar Samar Da Wutar Lantarkin Nijeriya Ta Sake Lalacewa A Karo Na 11
- Karin Kayayyaki Daga Kasashe Mafi Karancin Ci Gaba Sun Shiga Kasuwar Kasar Sin Ta Bikin CIIE
Kungiyar ta NMA ta ba gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 48 da ta sauke kwamishinar jin kai, ko kuma ta tsunduma yajin aiki, idan gwamnati ta gaza biyan bukatar ta.
Sai dai gwamnan wanda ya mayar da martani kan lamarin a yayin wani taron tattaunawa kai tsaye da wasu gidan rediyo a gidan gwamnati, ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin da NMA ta dauka bayan wata rashin fahimta da aka samu tsakanin mata biyu.
Gwamnan ya jaddada cewa, ya kamata kungiyar NMA ta bai wa kwamitin bincike da aka kafa damar gudanar da bincike kan lamarin tare da daukar kwakkwaran mataki, maimakon tsunduma yajin aiki wanda hakan zai iya jefa rayuwar mutane sama da miliyan 20 cikin hadari.