A baya bayan nan wasu ’yan siyasar kasar Amurka sun yi zargin cewa wai kasar Sin tana cika kasuwannin duniya da hajoji fiye da kima, don haka kamata ya yi Sin ta sake dadaita tsarin tattalin arzikinta. To sai dai kuma idan mun yi la’akari da dalilai na zahiri, za mu ga cewa wannan zargi ba shi da tushe bare makama. Kawai dai kokari ne na shafawa kasar Sin kashin kaji, musamman a wannan muhimmiyar gaba da ake ganin tattalin arzikin kasar Sin na kara shiga kyakkyawan yanayin ci gaba mai inganci.
Alal hakika, duk da cewa Sin na samar da tarin hajoji da ake fitarwa kasashen ketare, a daya hannun ana iya ganin yadda a shekarun baya bayan nan adadin hajojin kasar da ake fitarwa ketare na ta raguwa, kana Sin na kara fadada shigo da hajoji daga ketare, wadanda ya zuwa shekarar 2024 da ta gabata, darajarsu ta kai sama da dalar Amurka tiriliyan 2.64, adadin da ya ninka na shekara ta 2000 har sama da sau 10.
A yau, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na karuwa bisa dogaro da bukatun cikin gida. Har ma a shekarar 2024, alkaluma suka nuna yadda sayayya a cikin kasar ta samar da gudummawar sama da kaso 40 bisa dari na jimillar GDPn kasar, tare da zama daya daga manyan ginshikan bunkasa tattalin arzikin kasar.
Bugu da kari, Sin ta zamo babbar cibiyar raya bincike da fadada kere-keren masana’antu, wanda hakan ke kara jawo jarin waje zuwa cikin kasar, yayin da kuma sashen masana’antun kasar ke kara sauyawa zuwa mai samar da hajoji masu matukar inganci. Ana iya ganin hakan a fannin kera ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi, inda fitar da su da kasar Sin ke yi zuwa ketare ke taimakawa wajen sauya tsarin masana’antunsu a matakin kasa da kasa. Baya ga kera ababen hawa masu aikin da sabbin makamashi, Sin ta kuma zamo cibiyar bincike da gwaje-gwaje a wannan fanni.
Yayin da wasu ’yan siyasar Amurka ke ganin ya zama wajibi Sin ta sauya salon gudanar da tattalin arzikinta, a daya bangaren masharhanta na ganin hakan wani yunkuri ne kawai na ingiza ajandar nan ta raba-gari da Sin, wadda kuma ba za ta taba yin nasara ba. Domin ta hanyar gudanar da sahihin hadin gwiwa ne kadai sassan kasa da kasa za su iya cimma nasarar dunkule tattalin arzikinsu waje guda, ba wai ta hanyar cimma riba ta hanyar gurgunta ci gaban wani bangare ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp