Nasiru Buba, mijin da ya zargi kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara da yin tarayyar da ta bata kamata ba da matarsa, ya ki amincewa da hukuncin da wata kotu ta yanke na wanke kwamishinan daga aikata ba daidai ba.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wata babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Kano ta yi watsi da karar da ake yi wa Sankara a ranar Litinin din da ta gabata, saboda rashin samun hujjoji.
- Kotu Ta Wanke Kwamishinan Jigawa Daga Zargin Zina
- Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Tashar Mota Ta Zamani A Gusau
Alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola ya yi fatali da karar bayan da ya amince da rahoton ‘yansandan da ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa, Sankara ya aikata zargin da ake yi masa.
Da yake mayar da martani ga hukuncin, Buba ya bayyana hakan a matsayin rashin adalci, inda ya dage cewa ya bayar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da ikirarin nasa.
“Na gabatar da daruruwan shaidun da za a iya tantancewa, wadanda suka hada da hotuna 854, bidiyoyi fiye da 100, bayanan murya fiye da 200 a manhajar WhatsApp, da bayanan kiran waya na sama da sa’o’i 500. Idan kotu ta jefar da wadannan hujjoji, Allah da kuma mutanen da suka san gaskiya, ba za a goge su ba,” in ji Buba yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Lauyan Buba, Rabi’u Sidi, ya zargi kotun da jingine tawagar lauyoyin mai kara daga cikin shari’ar.
“Ba a sanar da mu zaman kotun ba. Babu wanda ya ce mana za a yi zama, kawai mun ji labarin hukuncin ne a cikin labarai,” in ji Sidi.
Ya kara da cewa tawagar lauyoyin za ta yi taro domin sanin matakin da za su dauka na gaba.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya mayar da Sankara kan mukaminsa bayan kotu ta wanke zargin da aka yi masa.
Umarnin mayar da Kwamishinan bakin aiki na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar ranar Talata.
Ibrahim ya ce, hukuncin ya biyo bayan wanke Sankara da wata kotun shari’a ta Kano ta yi kan zargin da ake masa.