Kwanan baya Zeljka Cvijanovic, shugabar karba-karba na kasar Bosnia da Herzegovina ta shedawa wakiliyar CMG cewa, muhimman dabarun raya tattalin arziki na kasar Sin abin koyi ne ga duniya, Bosnia da Herzegovina na iya koyan dabaru da fasaha daga matakai da shirye-shiryen da Sin take aiwatarwa, kuma daga baya a yi amfani da su bisa halin da yankin ke ciki, ta yadda za a samu ci gaban tattalin arziki da amfanawa kasarsa.
A cewar Zeljka Cvijanovic, kasashen biyu na kara yin mu’ammala da hadin kai, abin dake da ma’ana matuka ga kasar.
Tattaunawar da aka saba yi tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban, tun daga ziyara tsakanin jami’ai da mu’amalar jama’a a sassan tattalin arzikin kasashen biyu ta hanyoyi daban-daban, ya kafa tushe na zurfafa hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu a nan gaba. (Amina Xu)