Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Zhao Leji, ya kai ziyarar sada zumunta a kasar Kyrgyzstan daga ranar 23 zuwa 24 ga wata, inda ya gana da shugaban kasar Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov a birnin Bishkek.
Yayin ganawarsa da Japarov, Zhao Leji ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen tsakiyar Asiya ciki har da Kyrgyzstan, don inganta gina al’umma mai makoma bai daya tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya.
Japarov ya bayyana cewa, layin dogo tsakanin Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan, ba wai wata muhimmiyar hanyar sufuri ce kadai ba, har ma wata “hanyar abokantaka” ce dake sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin yankin.(Safiyah Ma)














