A ranar Alhamis ne Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta bukaci al’ummar Musulmi su kara kaimi wajen addu’o’ia ga kasar mu Nijeriya na neman karin zaman lafiya.
Wannan kiran na kunshe ne a sanarwar da Sakataren kungiyar, Dakta Khalid Aliyu ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai dangane da shigowar watan Zhul-Hijjah, watan Zhul-Hijjah ne wata ta 12 a jerin watannin Musulunci, kuma a watan ne da ake gabatar da ibadar yanka ragunan layya.
Mai Alfarma Sultan na Sakkwato, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya sanar da cewa, ranar Alhamis 30 ga watan Yuni ne 1 ga watan Zul-Hajji, ya kuma nuna muhimmancin kwanaki 10 na farkon watan.
Sarkin Musulmin ya nemi a kara kaimi wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya a sassan Nijeriya.
Sakataren kungiyar ya kuma ce, lallai akwai bukatar neman karin kariya daga sace-sace da kashe-kashen mutane da ake yi a sassan Nijeriya.
Ya kuma bayyana cewa, addu’o’in nada matukar muhimmanci musamman ganin muna fuskantar zabe a shekarar 2023.