Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince da fitar da Naira biliyan 1.3 a matsayin tallafin karatu ga daliban aikin jinya da unguwar zoma 997 daga jihar.
Zulum ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu a kwalejin koyon aikin jinya da unguwar zoma da ke Maiduguri.
- Mun Ceto Sama Da Mutane 1000 Ba Tare Da Biyan Kudin Fansa Ba – Ribadu
- Da Ɗumi-ɗuminsa: Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Fara Binciken Gwamnatin el-Rufai
Ya ce, daga cikin sunayen mutane 1,080, 40 daga kowace karamar hukuma 27 na jihar, 997 ne suka cancanci cin gajiyar tallafin.
Ya kuma bayyana cewa, dalibai 997 da suka ci gajiyar tallafin, za a basu takardar kama aiki da zarar sun kammala karatun.
Gwamnan ya ce, tallafin da aka bayar, an yi ne don karfafa wa daliban kwarin gwiwar kammala karatunsu ta yadda za a cike gibin gurbin ma’aikata a tsarin kiwon lafiya na jihar.