Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya bukaci sojojin Nijeriya da su kafa sansanin soji a dajin Sambisa, domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda yadda ya kamata.
Ya bayyana hakan ne a wata ziyarar ban girma da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan harkokin soji suka kai masa, ranar Laraba a Maiduguri.
- Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa A Farkon Bana
- Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Fitar Da Miliyan 309.5 Don Tallafawa Ɗaliban Da Ke Karatu a Ƙasashen waje
Gwamnan ya kuma bukaci sojojin da su kafa sansanin soji a gabar tafkin Chadi da kuma tsaunin Mandara wanda har yanzu ya ci gaba da zama mafakar ‘yan ta’adda.
Ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta tabbatar da samar da isassun makamai don magance rashin tsaro.