Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya jagoranci rabon tallafin abinci da gwamnatin tarayya ta bayar ga magidanra sama da 10,000 a ƙaramar hukumar Mafa jihar.
An gudanar da rabon kayayyakin ne a ranar Talata a cibiyoyi huɗu da ke garin Mafa, shalkwatar ƙaramar hukumar.
Kowane daga cikin magidantan dubu 10 ya samu tallafin kayan da abinci da suka hada da buhun masara mai nauyin kilogiram 50.
Zulum, ya nuna jin daɗinsa da godiya ga gwamnatin tarayya bisa wannan tallafi, tare da bayyana cewa an raba wasu kayan abinci a Gwoza da Nganzai.