Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno a ranar Asabar ya ziyarci garin Darajamal dake garin Bama domin jajantawa iyalan mutane 63 da mayakan Boko Haram suka kashe a daren Juma’a.
Wadanda abin ya shafa sun hada da sojoji biyar da fararen hula kusan 58.
Tun da farko, maharan sun raba mazauna garin da matsugunansu shekaru da dama amma gwamnati ta sake tsugunar da su a garinsu Darajamal watanni biyu da suka gabata.
Zulum, wanda ya yi matukar takaici da harin, ya gana da shugabannin al’umma tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp