Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta kara bai wa Nijeriya rancen wasu kudade da kuma zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a kasar.
Tuggar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da gidan Talabijin na Channels a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya kara da cewa, Nijeriya ba ta cikin kasashen da ke fama da bashin da ya yi katutu, don haka, ba ta tattauna batun yafe basussuka da kasar Sin ba.
- ‘Yan Kasuwa Daga Amurka Na Shirin Zuba Hannu Jari A Jihar Nasarawa – Gwamna Sule
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Ce Babu Rashin Fahimta Ko Shubuha Dangane Da Kuduri Mai Lamba 2758
A cewar ofishin kula da basussuka (DMO) na kasa, bashin da ake bin Nijeriya a ketare a watan Maris na 2024 ya kai Naira tirilyan 56 ($42bn) yayin da bashin cikin gida ya kai Naira tirilyan 65 ($46.29).
Da aka tambaye shi, ko Nijeriya na tattaunawa da kasar Sin kan batun yafe basussuka biyo bayan ganawar da shugaba Bola Tinubu ya yi da shugaban Sin, Xi Jinping a kwanakin baya? ministan ya ce, babu wani batun tattaunawa kan yafe basussuka.
Tuggar ya kara da cewa, kasar Sin ma tana son bai wa Nijeriya rancen kudade ne da kuma kara zuba jari a tattalin arzikin kasar.