Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, za ta gudanar da wata zanga-zanga ta kwanaki biyu a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairun 2024, saboda tsadar rayuwa da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a fadin kasar.
Shugaban kungiyar, Kwamared Joe Ajaero ne ya bayyana haka a hedikwatar kungiyar da ke Abuja, a wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
Ya ce, an yanke wannan shawarar ne domin nuna rashin amincewa da wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Cikakkun bayanai na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp