• English
  • Business News
Monday, May 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙungiyar Sadarwa Ta Ƙasa Ta Fitar da Sabbin Matakan Tallata Nasarorin Gwamnatin Tinubu

by Sulaiman
2 days ago
in Labarai
0
Ƙungiyar Sadarwa Ta Ƙasa Ta Fitar da Sabbin Matakan Tallata Nasarorin Gwamnatin Tinubu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ƙungiyar Sadarwa ta Ƙasa (National Communication Team) ta kammala taron duba yadda ta gudanar da ayyukan ta a tsakiyar wa’adin ta, tare da ɗaukar sababbin matakai na ƙara bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke samu.

Ƙungiyar ta ƙunshi hukumomi da jami’ai na Gwamnatin Tarayya waɗanda alhakin shelar ayyukan gwamnatin Tinubu ya rataya a wuyan su.

  • Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo
  • Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet

Taron ya gudana ne a Abuja ƙarƙashin jagorancin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a ranar Juma’a.

Labarai Masu Nasaba

Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

A sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkar yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya bayyana cewa a jawabin sa na buɗe taron, ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda haɗin kai ke ƙaruwa a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai a cikin gwamnatin.

Ya ce haɗin kan da daidaiton manufa sun ƙara inganta isar da saƙo da kuma fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu.

Ministan ya yaba da yadda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da shugabannin hukumomin yaɗa labarai da kuma mataimakan shugaban ƙasa a ɓangaren watsa labarai da dabarun sadarwa.

Ya ce wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen tabbatar da cewa saƙonnin gwamnati suna da tsari, suna dogara da hujjoji, kuma suna amsa buƙatun jama’a.

Ya jaddada cewa wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen gina amincewar jama’a da kuma ƙara wayar da su game da tasirin Ajandar Sabunta Fata a ɓangarori masu muhimmanci kamar tattalin arziki, ababen more rayuwa, lafiya, ilimi da ayyukan jinƙai.

Ministan ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da haɗa kai, tare da tabbatar da aiki cikin ƙwarewa, domin ƙara ƙarfafa wayar da jama’a kan nasarorin gwamnati a cikin gida da waje.

Ƙungiyar ta cimma matsaya kan a ƙara mayar da hankali wajen nuna nasarori a fannonin raya karkara, noma, gine-ginen ababen more rayuwa da kuma yaƙi da rashin tsaro, waɗanda su ne suka shafi rayuwar al’umma kai-tsaye.

Don ƙarfafa wannan yunƙuri, Idris ya buƙaci da a ci gaba da gudanar da tarurrukan tuntuɓa a jihohi da Babban Birnin Tarayya.

Ya ce tarurrukan tuntuɓar za su ba da damar tattaunawa kai-tsaye tsakanin wakilan gwamnati da jama’a, wanda hakan zai taimaka wajen gina amincewa, gaskiya da kuma gwamnatin da jama’a ke da tasiri a cikin ta.

Ƙungiyar ta bayyana aniyar ta ta ci gaba da yaɗa bayanai da za su ƙarfafa tattaunawar ƙasa, domin nuna tasirin ƙoƙarin gwamnati da kuma ƙarfafa haɗin kai da shiga cikin harkokin mulki.

Taron ya samu halartar shugabannin hukumomin yaɗa labarai da suka haɗa da Darakta Janar na NTA, Kwamared Abdulhamid Dembos; Darakta Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Malam Lanre Issa-Onilu; Darakta Janar na VON, Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta Janar na ARCON, Dakta Olalekan Fadolapo; da Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Jaridu ta Ƙasa, Dakta Dili Ezegha.

Sauran su ne Manajan Darakta na NAN, Malam Ali M. Ali; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Mista Bayo Onanuga; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Mista Sunday Dare; da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Dabarun Bayanai, Mista Daniel Bwala.

Haka zalika, akwai masu taimaka wa Shugaban Ƙasa da suka haɗa da Tope Ajayi (kan Harkokin Labarai), Abdulaziz Abdulaziz (kan Jaridu), Mista Otega Ogra (kan Sadarwar Zamani), Linda Akhigbe (kan Sadarwa ta Dabaru), da kuma Ali Audu (kan Harkokin Jama’a).

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

Next Post

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda

Related

Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato
Tsaro

Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

7 hours ago
Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato
Labarai

Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

8 hours ago
2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC
Labarai

INEC Na Samun Matsin Lamba Don Kar Ta Yi Wa TNN Rajista — Kakakinta

10 hours ago
Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa
Labarai

Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

11 hours ago
Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci
Ra'ayi Riga

Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci

11 hours ago
Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU
Labarai

Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU

12 hours ago
Next Post
Tinubu

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda

LABARAI MASU NASABA

A Koyi Darasi Daga Tarihi

A Koyi Darasi Daga Tarihi

May 11, 2025
Kada A Bata Ran Mahaifiya

Kada A Bata Ran Mahaifiya

May 11, 2025
Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

May 11, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

May 11, 2025
Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

May 11, 2025
Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

May 11, 2025
Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

May 11, 2025
2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC

INEC Na Samun Matsin Lamba Don Kar Ta Yi Wa TNN Rajista — Kakakinta

May 11, 2025
Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

May 11, 2025
Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu

Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu

May 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.