Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya ta fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasashen Afirika da kafar dama, bayan lallasa ƙasar Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga yau Lahadi a filin wasa na Prince Moulay Abdellah.
Asisat Oshoala da Rinsola Babajide da Chinwendy Ihezuo ne suka jefa kwallayen da suka yi sanadiyar samun nasarar ‘yan matan, yanzu Nijeriya ta dare teburin rukunin ‘B’ wanda ke ɗauke da ƙasashen Algeria da Botswana da Tunisia da Nijeriya.
- Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa
- Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka?
‘Yan matan da Madugu ke jagoranta za su haɗu da ƙasar Botswana a wasa na biyu, Nijeriya ce ƙasar da tafi lashe wannan gasar a tarihi yayin da ta lashe sau 9, Super Falcons kamar yadda ake kiransu tana fatan ganin sun dawo da wannan kofi zuwa gida Nijeriya, domin ragewa ‘yan ƙasar raɗaɗin rashin nasara a wasan ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika da aka buga a ƙasar Cote d’voire.
Yanzu dai tawagar za ta yi ƙoƙarin ganin ta ci gaba da samun nasarori yayin da take shirin tunkarar wasansu na gaba da ƙasar Botswana a ranar Alhamis, wannan nasarar ta aike da saƙo ƙarara ga sauran ƙasashen da ke buga gasar, wanda ke nuna matsayinsu na kasancewa kan gaba a gasar ƙwallon ƙafa ta mata a Afirka, da kuma ƙarfafa matsayinsu a matsayin ƙasar da ta fi samun nasara a tarihin WAFCON.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp