ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka?

by Abba Ibrahim Wada
1 year ago
Nahiya

Wasannin gasar FIFA Club World Cup da ake yi a Amurka ta yi nisa, domin an kammala wasannin rukuni daga nan a fara zagayen ‘yan 16. Duk da cewa ana samun korafe-korafe a gasar da suka hada da rashin cika filin wasa da zafin rana da sauransu, hakan bai hana kungiyoyin da suke buga gasar sun buga wasanni masu kayatarwa ba. A karon farko kungiyoyi 32 ke fafatawa a sabon fasalin Club World Cup da ya hada da 12 daga Nahiyar Turai da shida daga Kudancin Amurka da biyar daga Arewacin Amurka da hudu daga Afirka da hudu daga Asia da daya daga Nahiyar Oceania.

Tun farko an yi hasashen cewar kungiyoyin Turai ne za su mamaye wasannin, saboda karfin tattalin arzikin gasar da suke bugawa da ingancinsu da fitattun ‘yan kwallon da take da su. Daga ciki, akwai kungiyar Botafogo ta Brazil da ta yi nasara a kan Paris St German mai rike da Champions League da 1-0. Chelsea, wadda ta kashe kusan €1.5

  • Rawar Da ‘Yan Wasan Afirka Suka Taka A Gasar Premier Ta Ingila
  • Kofin Duniya 2026: Kasashen Da Suka Samu Tikitin Shiga Gasar Zuwa Yanzu

billion a kaka ukun da suka gabata ta sha kashi a hannun kungiyar Rio de Janiero wato Flamengo, inda kungiyar ta Brazil ta doke mai buga Premier League da ci 3-1. Sai dai Chelsea a ranar Laraba ta doke Esperence ta Tunisia da ci 3-0.

ADVERTISEMENT

Haka kuma an ci gaba da samun sakamakon ban mamaki da kungiyoyin Kudancin Amurka ke samu a FIFA Club World a Amurka, hakan ya sa ake ta tafka muhawara kan wace Nahiya ce kan gaba wajen iya kwallo tsakanin Turai da Kudancin Amurka? Da farko dai ana kashe dan karen kudi wajen sayen ‘yan wasa da gudanar da gasar kasashen Turai da ladan da kungiya za ta samu da kuma ingancin wasannin da yake burge masu bibiya sau da kafa.

Idan aka auna a matsakaicin kudin da kungiya ke biyan ‘yan wasa daga 12 da suke buga Club World Cup ya kai €737 million. Babu wata Nahiyar da ta kusan kamo Turai a yawan kashe kudi haka a harkar kwallon kafa. Sai Kudancin Amurka mai €154m, sannan Asia mai €60m, Arewacin Amurka ya kai €58m, Afirka kuwa ya kama daga €30m, yayin da Oceania, wadda take da kungiya, Auckland City matsaikaicin kudin da take biyan ‘yan wasa ya kama €5m.

LABARAI MASU NASABA

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare

To sai dai ana bibiyar kwallon kafa tsakanin magoya baya a Nahiyar Turai da Kudancin Amurka, sannan kowacce takan samar da fitattun ‘yan wasan da suke fice a nahiyar da kuma duniya a fannin kwallon kafa. Wannan yana biyo bayan zuba hannun jari da bunkasa wuraren wasan kwallon kafa da gasa mai inganci da kayatarwa musamman a Nahiyar Turai.

Nahiyar Turai ta lashe kofin duniya guda 12, idan ka kwanta da tara da Kudancin Amurka ta dauka a tarihi. Kungiyoyin Turai, musammam masu buga gasar English Premier League da Spanish La Liga da Bundesliga ko Serie A, sune suka mamaye lashe Champions League da kuma Club World Cup a tarihi.

Sannan nahiyar Turai tana zuba kudi da hannun jari a fannin ci gaban kwallon kafa ta matasa tun daga tushe, hakan ya sa kungiyoyinsu ba sa rasa ‘yan wasan da za su buga musu wasa, kuma masu inganci da kwarewa a manyan kungiyoyi.

Gasar wasan Turai tana da yanayi mai karfi a wasannin da ake yi, wanda mutane da yawa suka yi imanin tana da inganci da kayatarwa, hakan ya kan sa tawagar kasa kan yi kokari, duk lokacin da ta je babbar gasar kwallon kafa ta duniya.

Kudancin Amurka na da tarihin kwallon kafa, tare da fitattun ‘yan wasa irin su Pele da Maradona da Messi da sauransu da suka fito daga Kudancin Amurka. Ana matukar kaunar kwallon kafa a Kudancin Amurka. Kaunar kwallon kafa a kudancin Amurka kamar al’ada ce mai karfi, yadda ake kishin kungiya da yadda ake cika filayen wasa da samar da yanayi mai kayatarwa a lokacin da ake manyan wasanni.

Kudancin Amurka na ci gaba da samar da ‘yan wasa masu hazaka na musamman, amma yawancin ‘yan kwallon suna kaura zuwa Turai tun suna kanana, suna yin tasiri mai karfin a wasannin Turai, yayin da ake rashi daga Kudancin Turai. Idan za mu yi lissafin yawan samun maki a Club World Cup da ake bugawa a Amurka, Kudancin Amurka ce kan gaba da wasannin  da aka buka daga lokacin da aka hada wannan rahoton.

Mai biye da ita sai Nahiyar Turai, sannan sauran da suka bi baya a yawan hada maki a Club World Cup a bana. Tsakanin kungiya shida daga Kudancin Amurka, Botafogo ta samu maki shida, Flamengo maki bakwai, Fluminense maki bakwai, Riber Plate maki hudu, Palmeiras maki biyar da kuma Boca Juniors mai maki biyu, kenan jimilla maki 4.1.

Duk da Nahiyar Turai tana da kungiya 12 dake wakiltarta, tana da maki 48, idan kayi jimilla zai kai 4.00, kenan Kudancin Amurka ce kan gaba. Kenan za a samu kungiyoyin Kudancin Amurka da yawa da za su kai zagayen ‘yan 16, in ban da Boca Junior da ba ta yin kokari daga cikinsu kuma tuni ta fita daga gasar.

Nahiyar Afirka ce ta uku a kokari a Club World Cup mai matsakaicin maki 1.75, inda Mamelodi Sundowns ta hada maki hudu, sai Esperance Tunis mai maki uku da Al Ahly da Wydad Casablanca da ba su sami maki ko daya ba daga wasa biyu a cikin rukuni. Nahiyar Kudancin Amurka mai kungiya biyar ta samu matsaikacin maki 1.20, inda kungiyar Lionel Messi, Inter Miami ta samu maki biyar daga guda tara.

Nahiyar Asia ce ta biyar da maki 0.50, inda kungiyar Saudiyya, Al-Hilal ta samu maki biyu daga karawa uku kuma tuni ta fice daga gasar. Ta karshe ita ce Nahiyar Oceania mara maki, wadda aka durawa kungiyar New Zealand kwallo 16.

Za a iya cewa yayin da Kudancin Amurka ke da al’adar son kwallon kafa sau da kafa da kuma samar da ‘yan wasa na musamman ‘yan baiwa, Turai a halin yanzu tana kan gaba ta fuskar ingancin gasa, mai dan karen farin jini da kayatarwa sannan a Turai ana ci gaba da kokari wajen kawata wasannin kwallon kafa da fasahar zamani domin gujewa kuskuren alkalanci da kuma daidaita kashe kudade.

Nahiya
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu
  • Abba Ibrahim Wada
    Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?
  • Abba Ibrahim Wada
    Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji
  • Abba Ibrahim Wada
    Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

MASU ALAKA

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64
Wasanni

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

July 12, 2026
Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare
Wasanni

Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare

July 11, 2026
Wasanni

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

July 11, 2026
Next Post
Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?

Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.