Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya ta lallasa abokiyar karawarta Zambia a wasan kwata fainal na gasar ƙwallon mata ta ƙasashen Afirika.
Wasan wanda aka buga a filin wasa na Larbi de Zoubi dake birnin Casablanca ya matuƙar ƙayatar da ‘yan kallo musamman masu goyon bayan tawagar Nijeriya.
- Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700
- Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba
Osinaci Ohale ce ta fara buɗe ragar Zambia minti 2 kacal da fara wasan, Esther Okoronkwo ce ta jefa ƙwallo ta biyu, kafin Chinwendu Ihezuo ta jefa ƙwallo ta uku dab da zuwa hutun rabin lokaci.
Bayan an dawo hutun rabin lokaci Blessing Demehin ta ci ƙwallo ta 4 a wasan, ‘yan matan na Madugu sun ƙarƙare wasan da ƙwallon da Florence Ijamilusi ta ci a minti na 90, da wannan nasarar ne Nijeriya ta samu tikitin buga wasan na kusa da na ƙarshe na mafi ƙololuwar gasar ƙwallon mata a nahiyar Afirika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp