Rashin wutar lantarki ya sa an samu ƙarancin ruwan sha da ya jefa al’ummar Damaturu cikin mayuwacin hali.
Wani rahoto da LEADERSHIP ta ruwaito ya bayyana yadda ake fama da ƙarancin ruwan sha a unguwannin Alimarami da Ajari da kuma wasu wuraren da ke babban birnin jihar Yobe, saboda matsalar wutar lantarki da ake fama da ita.
- Ko Yanzu Tinubu Ya Yi Rawar Gani, Kuma Yana Ƙoƙari Sosai – Buhari
- Ramadan: Tinubu Ya Buƙaci Mawadata Da Su Taimakawa Mabuƙata
Wasu daga cikin mazauna yankunan da LEADERSHIP ta gana da su sun bayyana cewa, a halin yanzu matsanancin rashin ruwan ya kai ga mutane suna sayen duk baro ɗaya mai jarkoki 12 na ruwa kan naira 800 zuwa naira 1200.
Wani mazauni unguwar Alimarami mai suna Abdallah ya ce, suna sayen kurar mai jarka 12 kan N800 zuwa N1000.
Kazalika, wani mazauni Unguwar Ajari ya ce, a wurinsu kurar ruwa mai jarka 12 ana sayar da ita ne kan N1200.
Wannan yanayi da al’ummar Damaturu suka tsinci kan su ya sanya gwamnan jihar, Mai Mala Buni, ya bayar da umarnin kai man gas a dukkanin wuraren da ake samar da ruwan sha, domin kawo karshen matsalar.
Idan dai za a iya tunawa jaridar LEADERSHIP a watan da ya gabata ta ruwaito yadda wasu da ake zargi ƴan Boko Haram da lalata layukan da ke samar da lantarki da ta kai 330KV, wanda hakan ya saka al’ummar yankin cikin matsanancin halin rashin ruwa.