ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa

by Abubakar Sulaiman
10 months ago
Tsohuwar Firaministan Bangaladesh Sheikha Hasina,

Tsohuwar Firaministan Bangaladesh Sheikha Hasina,

Wata kotun ta musamman a kasar Bangladesh ta yanke wa tsohuwar Firaminista, Sheikh Hasina, hukuncin kisa a ranar Litinin bisa zargin aikata laifukan cin zarafin bil’adama da suka shafi zanga-zangar dalibai ta bara, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane kuma ta kawo ƙarshen mulkinta na tsawon shekaru 15.

Kotun ta kuma yanke wa tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Asaduzzaman Khan, hukuncin kisa, yayin da tsohon Sufeton ’Yansanda kuma ya samu hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar bayan ya amsa laifi.

  • Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a
  • Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Hukuncin, wanda aka karanta a babban birnin Dhaka, an watsa shi kai tsaye ta talabijin. Kafin hukuncin, gwamnatin rikon kwarya ta ƙara tsaurara tsaro a fadin ƙasar ta hanyar tura jami’an iyaka da yansanda musamman a Dhaka da sauran yankuna. Jam’iyyar Awami League ta Hasina ta sanar da rufe ƙasa baki daya a matsayin martani ga hukuncin.

ADVERTISEMENT

Hasina da Khan, wadanda ke gudun hijira yanzu haka a Indiya, an gurfanar da su ne ba tare da duk basa nan a kotun. Su da jam’iyyarsu sun yi watsi da kotun, suna kiran ta “kotun bogi,” tare da sukar lauyan gwamnati da aka nada musu. Zarge-zargen sun samo asali ne daga tarzomar dalibai a Yuli zuwa Agusta 2024 wacce ta yi sanadin mutuwar mutane da dama. Rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a Fabrairu, an kiyasta mutanen da suka mutu zuwa 1,400, yayin da wani jami’in kiwon lafiya na gwamnati ya ce sun zarce 800, inda kusan 14,000 suka ji rauni.

A makon da ya gabata, kotun ta tabbatar da ranar Litinin domin yanke hukunci bayan sake barkewar tashin hankali da suka haɗa da fashewar ƙananan bama-bamai da kone-kone da suka dakatar da makarantu da harkokin sufuri bayan jam’iyyar Awami League ta yi kira da a rufe ƙasa. Kafin yanke hukuncin, jam’iyyar ta sake nanata kiran rufe ƙasa, inda Hasina ta yi kira ga magoya bayanta ta cikin saƙon murya da kada su ji tsoro game da sakamakon.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

Bangladesh
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.