Abin da masana’antar Kannywood ke buƙata don ci gaba shi ne salon labari da zai isar da saƙo ga al’ummar duniya ba Hausawa kaɗai ba.
Wannan maganar na fitowa ne daga bakin fitaccen jarumin fina-finan Hausa da Turanci Muhammadu Rabi’u Rikadawa.
- Kalau Nake Babu Abin Da Ke Damun Kwakwalwata – Adam Zango
- Babu Inda Mayaudara Da Mahassada Suka Taru Kamar Masana’antar Kannywood – Adam Zango
Jarumin ya ce rashin salon tsara labari mai kyau da kuma wayewar harkar fina-finai a masana’antar Kannywood ita ke hana masu zuba jari da ɗaukar nauyin wasu daga cikin fina-finan masana’antar
Cikin wata hirarsa da kafar gidan Jaridar Daily Trust, Rikadawa ya bayyana buƙatar masu ruwa da tsaƙi su sauya tsarin yadda suke tafiyar da masana’antar Kannywood ɗin ta yadda za ta jawo hankalin masu zuba jari, wanda ya ce muddin ba a yi haka to masana’antar za ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta bunƙasa.