Alkaluma daga hukumar kula da makamashi ta kasar Sin sun nuna cewa, an samu karuwar karfin makamashi mai tsafta da kasar Sin ta shigar a cikin watanni hudu na farkon bana.
Ya zuwa karshen watan Afrilu, karfin wutar lantarki bisa karfin iska, ya karu da kashi 12.2 cikin 100 a shekara zuwa kusan kilowatt miliyan 380, yayin da karfin makamashi bisa hasken rana, ya kai kilowatt miliyan 440, karuwar kashi 36.6 kan na shekarar bara.
Kasar Sin ta kara zuba jarin da take yi a fannin makamashin da ake iya sabuntawa tsawon shekaru, a kokarin da take yi na samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp