Kasa da sa’o’i 30 da rasuwar mahaifiyarsa, Gwamna Umar Namadi ya sake rasa babban dansa, Abdulwahab Umar Namadi, wanda ya rasu a wani mummunan hatsarin mota a ranar Alhamis.
Hatsarin ya afku ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, 2024, a kauyen Agura mai kasa da kilomita uku zuwa garin Kafin Hausa, mahaifar gwamnan.
Abdulwahab da abokinsa na kan hanyarsu ta zuwa Kafin Hausa daga Dutse, babban birnin jihar, domin ci gaba da karbar ta’aziyyar rasuwar kakarsa, marigayiya Hajiya Maryam Namadi, a lokacin da hatsarin ya afku.