Ƙasar Sin ta ƙaddamar da shirinta na bidiyo mai suna “Kwaɗon Baka” a Nijeriya, domin bunƙasa dangantaka a tsakanin Nijeriya da ƙasar Sin.
Kwaɗon baka shiri ne na bidiyo da ƙasar Sin take gabatarwa a harshen Hausa da ke nuna al’adunta da kayayyakin tarihi da kaɗe-kaɗe da raye-raye domin ilmantar da al’ummar duniya a harshen Hausa.
Bikin ya gudana ne a cibiyar ƙasar Sin da ke Babbar Birnin Tarayya Abuja, wanda ya samu halartar ɗimbin baƙi na cikin gida Nijeriya da kuma ƙasar Sin.
An ƙaddamar da aikin ɗaukar shirin bidiyon kwaɗon baka bisa haɗin gwiwa a tsakanin rukunin kafafen yaɗa labarai na ƙasar Sin (CMG) da kuma gidan talabijin na ƙasa (NTA).
Da yake gabatar da jawabi wajen ƙaddamarwar, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed idris ya bayyana cewa ya yi farin cikin halartar wannan biki na gabatar da wannan shirin wanda haɗin gwiwa ne tsakanin NTA da CMG na China.
Ministan wanda ya samu wakilcin daraktan ma’aikatar yaɗa labarai, Dakta Sulaiman Haruna, ya ƙara da cewa haƙiƙa wannan shiri zai ƙara inganta dangantaka tsakanin tashosin talbijin na Nijeriya da rukunin kafafen yaɗa labarai na ƙasar Sin, kuma wannan wani ɓangare ne na jaddada hulɗar dangataka tsakanin al’ummar Nijeriya da ƙasar Sin, ta fuskar yaɗa al’adu da harsunan ƙasashen biyu, da sauran kafafen sadarwa na zamani da ke ƙasashen.
A cewarsa, gidajen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen sanya al’umma bisa hanya madaidaiciya, domin kawo fahimtar juna da samar da ingantaccen ci gaba, saboda haka ya ce gidajen yaɗa labarai na da kyakkyawar rawar da za su taka wajen ƙara inganta harkar zamantakewa, ci gaban tattalin arzikin ƙasa da bunƙasa al’adu da ke buƙatar ganin an sanar da mutane.
“Ina mai jinjina ga hukumomin watsa labarai na Sin da kuma hukumar talibijin ta ƙasa (NTA), saboda rawar da suke takawa wajen samar da sahihan labarai da shirye-shirye masu ma’ana da suke gabatarwa domin ci gaban ƙasashen biyu.
“Akwai buƙatar daidaito a wajen ba da labarai, musanman wajen faɗin irin ci gaba da nasarorin da ƙasar nan ta samu da kuma samar da shirye-shirye da za su ƙara wa masu tasowa kyakkyawan fata nan gaba.
“Nijeriya tana da matasa masu himma da ke ƙoƙarin aiki tukuru wajen ganin sun yi amfani da damarsu duk da irin ƙalubalen da suke fuskanta. Wasu daga cikin manyan ƙalubalen da matasa ke fuskanta a ƙasar nan da sauran ƙasashen duniya shi ne, yadda ake samun yaɗuwar labaran ƙanzon kurege da jita-jita da labaran ƙarya wanda ya kawo koma-baya da kuma rashin yarda tsakanin gwamnati da al’umarta.
“Yana da muhimmanci ga kafofin yaɗa labarai na ƙasar Sin su taimaka wajen magance wannan matsala ta hanyar yin aiki tare da sauran takwarorinsu na ƙasashen duniya domin su kawo ƙarshen wannan mummunar ɗabi’a da tabbatar da cewa kafafen yaɗa labarai sun ci gaba da zama abin dogaro da nuna sanin ya kamata.
“Akwai buƙatar ƙasar Sin ta ƙara faɗaɗa tashohinta a Nijeriya ta hanyar ƙara sanya wasu harsuna da suka haɗa da Hausa da Igbo da Yoruba da Pidgin domin isar da saƙonni da samar da ayyukan yi da horas da ‘yan Nijeriya.” In ji ministan.
A nasa jawabin, babban jami’in kula da ɓangaren al’adu na ofishin jakadancin ƙasar Sin da ke Nijeriya, Li Xuda ya bayyana cewa Nijeriya da ƙasar Sin suna da daɗaɗɗiyar hulɗa ta hanyar bunƙasa al’adu da tattalin arziki da da dai sauran fannoni masu yawan gaske.
Ya ce a farkon shekara ta 2022, an yi ganawa a tsakanin Nijeriya da Sin ta ɓangaren al’adu da harkokin yawon buɗe ido, wanda aka tattauna kan nasarorin da ƙasashen biyu suka samu a ɓangaren al’adu da yawon buɗe ido, sannan an amince a ci gaba da hulɗar bunƙasa al’adu a tsakanin ƙasashen biyu.
Har ila yau, mataimakiyar shugaban sashin Hausa na CMG, Kande Gao ta ce ƙaddamar da wannan shirin a Nijeriya ya zama wani gagarimin biki wurinta da kuma al’ummar ƙasar Sin.
Ta ƙara da cewa, bisa binciken da suka gudanar, wannan shiri ya samu matuƙar amsuwa, musamman a Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka, inda hakan ta ƙara ba su ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da aiwatar da ayyukan da suke yi.
Shi kuwa a nashi ɓangaren, shugaban gidan talabijin na NTA, Malam Salihu A. Dembos ya ce wannan ba ƙaramin abin alfari ba ne a ce ƙasar Sin ta ƙaddamar da shirinta a Nijeriya.
Shugaban na NTA wanda shugaban sashin Hausa na NTA, Aminu Isiyaka Abbas ya wakilta, ya ce lallai za su yi duk wani abu mai yiwuwa wajen bunƙasa wannan alaƙa ta al’ada a tsakanin Nijeriya da ƙasar Sin.
Daga cikin abubuwan da suka ƙayatar a wurin bikin ƙaddamar da shirin na Kwadon Baka dai har da nuna wasu wasanni na al’adun Sinawa.