Hukumar Kare Hakkin masu sayen kayayyakin more rayuwa ta Tarayya (FCCPC) ta bai wa ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci wa’adin wata daya da su sauke farashin kayayyaki.
Sabon shugaban hukumar FCCPC da aka nada, Mista Tunji Bello, ya bayyana haka a wani taron kwana daya da masu ruwa da tsaki suka yi kan hauhawar farashin kayayyaki a ranar Alhamis a Abuja.
- Sin Da Afrika Sun Samu Ci Gaba Mai Armashi Wajen Aiwatar Da Shawarar BRI
- Ƴansanda Sun Sallami Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago Ajaero Bayan Amsa Gayyatarsu
Talla
A cewar Bello, hukumar za ta fara daukar mataki da zarar wa’adin da aka gindaya ya cika.
Ya ce, taron an yi shi ne don magance karuwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi da ke ci gaba da ta’azzara a kasar.
Talla